Isa ga babban shafi

Magoya bayan zakaran Tennis Rafael Nadal sun shiga rudani bisa rashin lafiyar sa

Magoya bayan zakaran wasan Tennis na Duniya dan kasar Spain Rafael Nadal, sun shiga rudani, bayan da suka samu labarin cewa ba zai buga Monte carlo ba.

Rafael Nadal après sa défaite contre l'Australien Jordan Thompson au tournoi de Brisbane, le 5 janvier 2024.
Rafael Nadal après sa défaite contre l'Australien Jordan Thompson au tournoi de Brisbane, le 5 janvier 2024. © AFP / PATRICK HAMILTON
Talla

Bayan da wasu rahotanni daga kasashen Spain da Italy ke cewa zakaran wasan ba zai halacci gasar Tennis ta maza ta Duniya ba, da ake yi duk shekara wato Monte Carlo, sakamakon fama da matsanancin ciwon ciki da baya.

Tun a ranar 23 ga watan Maris din daya gabata ne magoya bayan zakaran tennis din suka daina ganin motsinsa a kafafen sada zumunta, dalilin ma da ya sanya bayan fitar rahotannin suke cewa lallai biri ya yi kama da mutum.

Dan wasan ya jima bai yi wasa ba, tun bayan da ya samu rauni a gasar Australian Open ta 2023, wadda aka gudanar a kasar Australia daga ranar 16 zuwa 29 ga watan Janairun 2023.

Novak Djokovic dai shi ne ya lashe gasar bayan lallasa abokin karawarsa Stefanos Tsitsipas a wasan karshe da ci 6–3, 7–6, 7–6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.