Isa ga babban shafi

Na so kashe kai na lokacin da na yi rashin nasara a Wimbledon- Kyrgios

Zakaran kwallon Tennis na Australia Nick Kyrgios ya amsa cewa tabbas da gaske ne sai da ya yi yunkurin kashe kansa bayan rashin nasararsa a gasar Wimbledon cikin shekarar 2019, lamarin da ya kai shi ga doguwar jinya a asibitin masu tabin hankali da ke birnin London.

Zakaran kwallon Tenni na Australia Nick Kyrgios.
Zakaran kwallon Tenni na Australia Nick Kyrgios. AP - Hamish Blair
Talla

Matashin dan kwallon na Tennis Kyrgios mai shekaru 28 ya bayyana cewa bayan da Rafael Nadal ya doke shi a wasan na karshe yayin gasar ta Wimbledon sai da ya tsani kansa ta yadda ya ji cewa mutuwa kadai ce ta dace da shi.

A cikin wata doguwar hira da aka yi dashi kan halin da ya shiga bayan shan kayen ya ce a wancan lokaci ya tsinci kansa a halin shaye shayen kwayoyi ta yadda ya tsani kansa gabaki daya gabanin kwantar da shi a asibitin na London tare da taimaka masa wajen dawowa hayyacin da shawarwarin kwararru da kuma magungunan magance damuwa.

Kyrgios wanda ya samu nasara a wasan karshe na 2022 bayan murmurewa daga halin da ya tsinci kansa, ya ce ko kadan baya son tuna abin da ya faru da shi ko da ya ke ya bar zanen Tatto a jikinsa ta yadda zai rika tunawa da abin da ya faru da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.