Isa ga babban shafi

Na matukar kaduwa da labarin ritayar Nadal daga fagen Tennis- Djokovic

Zakaran kwallon Tennis na Duniya Novak Djokovic ya ce ya shiga damuwa matuka bayan ya ji kalaman takwaransa Rafael Nadal kan yiwuwar ritaya daga fagen na Tennis nan gaba kadan.

Novak Djokovic yayin wasan sa a gasar French Open.
Novak Djokovic yayin wasan sa a gasar French Open. AP - Jean-Francois Badias
Talla

A cewar Djokovic mai shekaru 36 da ke tunkarar nasarar lashe kyauta ta 23 a gasar French da ke ci gaba da gudana, ko shakka babu samun wannan labari game da Nadal ya sanya shi tunanin lokacin da zai yi ritaya daga fagen.  

Zakaran na Tennis dan Serbia ya ce lura da shekarun da suka shafe suna haskawa tare da Nadal a gasar ta Tennis, ritayarsa babbar manuniya ce a gareshi ta cewa shima lokacinsa ya kawo karshe.

A cewar Djokovic lokacin da Nadal ke sanar da Shirin ritaya sai ya ji tamkar wani bangare na jikinsa na rabuwa da shi

Nadal dai ya yi nasarar lashe kyautar Roland Garros karo na 14 amma kuma ya gaza kaiwa ga Grand Slam karon farko cikin shekaru 19 sakamakon ciwon kugun da ya ke fama da shi, ciwon da shi ya tilastawa dan wasan na Spaniya sanar da shirin ritayar.

Rafael Nadal mai shekaru 36 ya ce sai a shekarar 2024 ne zai yi bankwana da masoyanshi bayan sanar da ritayarsa a hukumance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.