Isa ga babban shafi

Djokovic ya koma matsayinsa na lamba 1 a fagen Tennis bayan lashe Australian Open

Zakaran kwallon Tennis na Duniya Novak Djokovic ya lashe kofin Australian Open karo na 10 a tarihi, bayan da ya doke Stefanos Tsitsipas dan kasar Girka da ci 6-3, 7-6, 7- 6 da kuma 7-5. 

Novak Djokovic dan Serbia ya koma matsayinsa na lamba daya a fagen Tennis na Duniya.
Novak Djokovic dan Serbia ya koma matsayinsa na lamba daya a fagen Tennis na Duniya. AP - Asanka Brendon Ratnayake
Talla

Bayan nasarar ta jiya, Novak Djokovic dan kasar Serbia mai shekaru 35 ya kamo takwaransa na Spain wato Rafael Nadal yawan manyan kofunan gasar Grand Slams, inda ya lashe na 22. 

Yanzu haka dai Djokovic ya koma matsayinsa lamba daya a fagen Tennis bayan rasa wannan matsayi a bara sakamakon gaza fafatawa a gasar ta Australian Open.

Australia dai ta tiso keyar Novak Djokovic a bara saboda abin da ta kira karya dokokin dokar corona bayan da ya shiga kasar ba tare da karbar allurar rigakafin cutar ba, inda aka bashi zabin ko dai ya karbi allurar ko kuma ya rasa damar haskawa a gasar kuma da wasan ya zabe hakura da gasar.

A wancan lokaci dai mahukuntan kasar sun sanya masa haramcin shekaru 3 na samun visa saboda karya doka gabanin janye matakin daga bisani.

Duk da cewa har a yanzu Djokovic bai amince da karbar allurar rigakafin cutar ta Corona ba anga yadda ya bayar da mamaki dawowa da kanbunsa tare da komawa matsayin da ya ke a baya da karin kyautar Grand Slam guda.

Bayan nasara a wasan na jiya kan Stefanos Tsitsipas, Djokovic ya kwaikwayi salon murnar dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford inda ya nuna kanshi da hannu, salon murnar da tuni wasu daga cikin 'yan wasan kwallon kafa da na kwando ke kwaikwayo.

Shi ma dai Rashford ya wallafa hoton Djokovic a shafinsa na Instagram tare da bayyanashi da gwarzo baya ga taya shi murna. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.