Djokovic ya sha kashi wasan karshe na Paris Masters
Matashin dan wasa an kasar Denmark Holger Rune bya bai wa Novak Djokovic mamaki a wasan karshe na gasar Paris Masters, inda ya lashe kofin a karon farko a sana’arsa.
Wallafawa ranar:
Dan wasan mai shekaru 19 ya hana Djokovic taka rawar gaban hantsi, inda ya hana shi lashe kofin Masters na Paris karo na 7 ta wajen doke shi 3-6 6-3 7-5.
Yanzu ya kasance dan wasa mafi karancin shekaru da ya lashe wannan gasa ta Paris tun bayan da Boris Becker ya lashe a shekarar 1986.
Wannan nasarar za ta kai Rune matsayi na 10 a jerin ‘yan wasan Tennis na duniya a karon farko idan aka wallafa sunayen ‘yan wasan a ranar Litinin din nan.
Djokovic ya taya matashin murna, inda ya ce yaro ne mai kuzari da sadaukarwa wanda ya cancanci nasarar da ya samu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu