Isa ga babban shafi
Wasanni - Tennis

Kwallon tennis: Djokovic ya fara gasar da gagarumar Nasara

Lamba daya duniya a fannin wasan kwallon Tennis, Novak Djokovic ya fara wasan kare kambunsa a gasar  French Open  da gagarumar nasara a kan dan kasar Japan, Yoshihito Nishioka.

 Novak Djokovic.
Novak Djokovic. AFP - MIKE FREY
Talla

Djokovic dan kasar Serbia ya yi nasara a wasan ne da ci 6-3 6-1 6-0 a da’irar wasan tennis ta  Court Philippe Chatrier.

Wannan ce babbar gasar Djokovic ta farko tun bayan da hukumomin Australiya suka tisa keyarsa gida gabanin gasar Australian Open a watan Janairu, bayan da ya ki amincewa da allurar rigakafin cutar COVID 19, lamarin da ya sa ya rasa damar kare kambunsa a gasar.

Tun da farko, shahararren dan kwallon tennis, Rafael Nadal ya lallasa  Jordan Thompson  da ci 6-2 6-2 6-2.

A wasansa na gaba, Djokovic zai hadu ne da dan kasar Argentina Federico Coria ko kuma dan kasar Slovakia Alex Molcan, wanda ke samun horo daga koci, Marian Vajda, wanda ya taba horar da Djokovic.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.