Isa ga babban shafi
Wasanni - Tennis

Djokovic zai rasa matsayinsa na lamba daya a kwallon Tennis

Novak Djokovic zai rasa matsayin na lamba day ana duniya a wasan kwallon tennis bayan da ya sha kashi 6-4 7-6 (7-4)  a hannun Jiri Vesely, a wasan daf da kusa da karshe na gasar Dubai Championships.

Novak Djokovic.
Novak Djokovic. © Chine Nouvelle / Sipa
Talla

Wannan gasa dai it ce ta farko da Djokovic ya buga a wannan shekarar ta 2022, bayan da aka hana shi fafatawa a gasar Australian Open sakamakon rashin karbr allurar rigakafin  Covid-19.

A ranar Litinin mai zuwa, za a maye gurbin dan kasar Serbia din da Daniil Medvedev a matsayin lamba daya na wasan kwallon Tennis na duniya.

Vesely, dan kasar Jamhuriyar  Czech wanda shine lamba na 123 a duniya a wasann Tennis, ya bayyana mamakinsa da nasarar da ya samu a kan lamba daya na duniya.

 Medvedev, dan kasar Rasha, zai kasance dan wasa na farko, wanda ba Djokovic, Roger Federer, Rafael Nadal ko Andy Murray ba da ya haye zuwa wannan matsayi a cikin shekaru 18.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.