Isa ga babban shafi
Tennis

Novak Djokovic zai bude gasar Wimbledon

A yau Litinin ne a za’a bude gasar kwallon Tennis ta Wimbledon a Birtaniya, kuma zakaran wasan na Duniya mai rike da kambun Novak Djokovic yana cikin ‘Yan wasan da zasu bude gasar a yau inda zai kara da tsohon zakaran gasar Rolland Garros Juan Carlos Ferrero.

Dan kasar Serbia Novak Djokovic Zakaran wasan Tennis na Duniya
Dan kasar Serbia Novak Djokovic Zakaran wasan Tennis na Duniya REUTERS/Giampiero Sposito
Talla

Tun bayan da Novak Djokovic ya sha kashi hannun Rafeal Nadal wasan karshe a gasar Roland Garros a makwanni biyu da suka gabata, Djokovic bai sake shiga wata gasa ba. Kuma wannan ne ya hana dan wasan lashe kofunan manyan gasar Tennis guda hudu na duniya a jere.

A bangaren mata kuma mai rike da kambun, Maria Sharapova da ta lashe Roland Garros za ta kara ne da Anastasia ‘Yar kasar Australia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.