Isa ga babban shafi
Wasanni -Tennis

Djokovic ya ce ba wanda ya isa ya tilasta masa karbar rigakafin Covid-19

Novak Djokovic ya  ce ya gwammaci a yi babu shi a  duk wata gasar Tennis da za a yi nan gaba da a tilasta masa karbar rigakafin Covid-19.

Novak Djokovic, dan wasan tennis lamba daya na Duniya.
Novak Djokovic, dan wasan tennis lamba daya na Duniya. Greg WOOD AFP/Archives
Talla

A wata ganawa da manema labarai, Djokovic ya ce kada a danganta shi da kungiyar masu adawa  da rigakafi, amma kuma ya goyi bayan dama da mutum yake da ita ta yin zabi.

Da aka tambayi Djokovic ko zai iya hakura da shiga gasa kamar su Wimbledon da French Open saboda ra’ayinsa a kan rigakafi, sai ya kada baki ya ce, ‘kwarai, abubuwa ne da na yi niyyar sadaukarwa.

A watan da ya gabata ne hukumomin Australia suka tisa keyar dan wasan da ya lashe manyan kofunan Grand slam sau 20  gida, sakamakon sa in sa a game da tirjewarsa a kan rigakafi, duk da cewa ya karbi izinin likita na shiga kasar bayan da ya murmure daga cutar covid da ta kama shi.

Dan wasan wanda shine lamba daya a wasan Tennis ya ce ya kafe a kan haka ne saboda yanke shawara a kan abin da ya shafi jikinsa ya fi masa duk wata lambar yabo ko kudi da zai samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.