Isa ga babban shafi
Wasanni

Djokovic ya fice daga gasar US Open

Zakaran kwallon Tennis na duniya, Novak Djokovic ya fice daga gasar US Open da ke ci gaba da gudana can a birnin New York bayan wata fusata da ya yi da ta kai shi ga buka kwallo da karfi wadda kai tsaye ta samu alkaliyar wasa sakamakon rashin nasararsa a karawarsa ta zagayen ‘yan 16, batun da ya tayar da hankalin masu kallo dama wadanda ke cikin gasar baya ga mahukuntanta.

Le Serbe Novak Djokovic disqualifié de l'US Open pour avoir envoyé une balle sur une juge de ligne.
Le Serbe Novak Djokovic disqualifié de l'US Open pour avoir envoyé une balle sur une juge de ligne. Danielle Parhizkaran-USA TODAY Sports
Talla

Zakaran kwallon na Tennis tuni ya bayar da hakuri tare da neman yafiyar magoya bayansa da ita kanta alkaliyar game da abin da ya faru.

Tun farko dai lamba dayar a fagen Tennis ya fusata ne dai dai lokacin da kwallo ta kubce masa a karawarsa da Pablo Carreno Busta na Spain ana wasa 6-5, dalilin da ya sanya shi dukan kwallon da karfi wadda kuma ta bugi alkaliyar wasa Soeren Friemel, wadda ta warwas gabanin akai mata dauki da taimakon lumfashi.

Tawagar alkalan wasan gasar ta US Open ne dai suka tsayar da maganar cewa Pablo ya lashe wasan tare da yin waje da Djokovic, inda nan ta ke zakaran kwallon na Tennis ya daga hannun sallama ga ‘yan kallo amma ba tare da musafaha da abokin karawar tasa ba, ba kuma tare da sauraron manema labarai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.