Isa ga babban shafi

Djokovic ya tsallake rijiya da baya a gasar Wimbledon

Novak Djokovic samu kaiwa zagayen wasan kusa da na karshe a gasar Wimbledon bayan tsallake rijiya da baya a fafatwar da yayi da Jannik Sinner na kasar Italiya a ranar Talata.

Novak Djokovic dan kasar Serbia yayin murnar doke Jannick Sinner na Italiya a zagayen kwata final na babbar gasar tennis ta Wimbledon dake gudana a Ingila.
Novak Djokovic dan kasar Serbia yayin murnar doke Jannick Sinner na Italiya a zagayen kwata final na babbar gasar tennis ta Wimbledon dake gudana a Ingila. AP - Alastair Grant
Talla

An dai shafe tsawon lokaci ana fafatawa tsakanin ‘yan wasan biyu har zagaye biyar, inda a zagaye biyun farko Djokovic ya sha kaye da 5-7, da kuma 2-6.

Sai dai kuma daga zagaye na uku zuwa na biyar Djokovic dan Serbia ya doke Sinner da 6-3, 6-2 da kuma 6-2.

A ranar Juma'a dan wasan na kasar Serbia zai kara da Cameron Norrie dan Birtaniya wanda ya samu nasarar kaiwa zagayen wasan kusa da na karshe na babbar gasar ta Wimbledon dake gudana a Ingila, bayan doke David Goffin dan kasar Belgium da 7-5,7-5 da kuma 6-3, sai kuma 2-6 da 3-6  bayan shafe zagaye 5 suna fafatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.