Isa ga babban shafi

Djokovic ya kafa sabon tarihi bayan lashe kyautar Grand Slam karo na 23

Novak Djokovic ya sake kafa tarihi a fagen Tennis bayan lashe kyautar Grand Slam karo na 23 a gasar French Open can a birnin Paris, wanda ya bashi damar zamowa gagarabadau a fagen.

Zakaran kwallon Tennis na Duniya, Novak Djokovic.
Zakaran kwallon Tennis na Duniya, Novak Djokovic. © Pierre René-Worms / RFI
Talla

Djokovic dan Serbia mai shekaru 36 ya yi nasarar ne bayan lashe dukkanin zagaye 4 na wasansa na karshe da ya doka da Casper Ruud na Norway da ci 7-6 7-1 da 6-3 da kuma 7-5 a Roland Garros, nasarar da ta bashi damar shigewa gaban Rafael Nadal wanda ke da Grand Slam 22.

Nasarar ta Djokovic na matsayin karo na 3 da ya samu makamanciyarta bayan lashe gasar ta French Open a birnin Paris wato a shekarun 2016 da 2021 da kuma yanzu 2023 yayinda ya lashe kofunan Tennis 10 a Australian Open kari kan wasu 7 a Wimbledon can a Amurka karkashin gasar US Open.

Zakaran kwallon na Tennis ya zama mutum na farko da ya lashe dukkanin manyan gasar Tennis na Duniya sama da sau 3 kowaccensu a tarihi inda ya tasamma goge duk wani tarihin gasar ko kuma kyautar ta Grand Slam da aka faro bayar da ita a 1969 karkashin Rod Laver.

A kaf gasar ta Tennis dai ‘yan wasa irinsu Margaret Court da Serena Williams kadai ke da kyautukan Grand Slam dai dai da Djokovic wanda kuma ake ganin zai tunkari goge tarihinsu a gasar Wimbledon da ke tafe cikin wata mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.