Isa ga babban shafi

Roger Federer zai yi murabus daga tennis a Juma'a

Roger Federer ya tabbatar da cewa zai yi ban kwana da wasan kwallon tennis a gobe Juma’a, bayan wasan ‘yan wasa 2 na gasar Laver Cup a birnin Landan.

Roger Federer ya lashe manyan kofunan Grand Slam 20.
Roger Federer ya lashe manyan kofunan Grand Slam 20. AP - Aaron Favila
Talla

A makon da ya gabata ne dan wasan, wanda sau 20 yake lashe babban kofin tennis na Grand Slam ya ce zai yi murabus.

Dan wasan ya yi fama da rauni a gwiwarsa, don haka zai yi mai wahala ya buga wasan mutum guda.

Wasan Federer na karshe a wata gasa ita ce wanda ya yi rashin nasara a hannun Hubert Hurkacz a gasar Wimbledon a shekarar da ta wuce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.