Isa ga babban shafi

Alcaraz ya dakile fatan Djokovic na lashe gasar Wimbledon karo na 8

Novak Djokovic ya fashe da kuka a tsakar fili bayan rashin nasararsa a hannun Carlos Alcaraz a wasan karshe na gasar Wimbledon wanda ya hana shi damar sake lashe kofin gasar karo na 8 a tarihi.

Novak Djokovic bayan shan kaye a hannin Carlos Alcaraz.
Novak Djokovic bayan shan kaye a hannin Carlos Alcaraz. AP - Alberto Pezzali
Talla

Djokovic wanda ya lashe Wimbledon sau 7 a tarihi ya yi fatan samun damar lashe kofin a wannan karon don yin kankankan da takwaransa Roger Federer tare da kamo Margaret Court a yawan kyautukan Grand Slam 24.

Lokacin da ake mika masa lambar yabo a matsayin wanda ya zo na biyu, cikin kwalla, Djokovic ya ce sai yanzu ya fahimci bacin ran da abokanan karawarsa ke fuskanta a gasar shekaru 4 da suka gabata.

Rabon Djokovic dan Serbia mai shekaru 36 da rashin nasara a irin wannan gasa a London tun shan kayensa a hannu Andy Murray cikin shekarar 2013, inda ya ce abin takaici ne yadda fatansa na lashe gasar karo na 8 ya zo da rashin nasara.

Alcaraz dan Spain mai shekaru 20 ya doke Djokovic ne a zagaye 5 da kwallaye 1-6, 7-6, 6-1, 3-6, 6-4 kuma ita ce nasara ta biyu da matashin dan Tennis din ya yi kan Novak amma kuma karon farko a London duk da yadda dan kasar ta Serbia ya mamaye gasar tsawon shekaru.  

Lura da yadda Djokovic ya shafe tsawon shekaruludayinsa na kan dawo a bangarewasan na Tennis a kusan dukkanin gasa kama daga Wimbledon, US Open ko Australian Open ko kuma French Open za a iya cewa yanzu lokaci ne na Alcaraz wanda ke matsayin lamba daya a wannan fage.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.