Isa ga babban shafi

Damben zamani: Viddal ya ce zai nuna wa Chamberlain ruwa ba sa’an kwando ba ne

Dan wasan damben zamanin nan Viddal Riley ya ce a shirye ya ke ya dambata da abokin hamayyarsa Isaac Chamberlain domin nuna masa ruwa ba sa’an kwando ba ne.

La Gaza Boxing Women attire de plus en plus d'adeptes. (Image d'illustration)
La Gaza Boxing Women attire de plus en plus d'adeptes. (Image d'illustration) © CC0 Pixabay/Contributeur
Talla

Kalaman na Viddal na zuwa ne bayan nasarar da ya samu a karshen mako akan abokin karawarsa Mikel Lawal da ci 11 da 0.

Nasarar ta sa ta zo ne watanni biyar da shima Chamberlain ya yi galaba akan Lawal lamarin da ya bashi damar zama zakaran damben boxing na kasashe rainon Birtaniya.

Chamberlain da Riley sun soma cacar bakin ne bayan sun hadu a fagen gasar damben da ta gudana ranar lahadin da ta gabata,.

Wannan dalili ne ya sanya kowannen su ke cin alwashin yiwa abokin karawarsa siri daya kwale muddun dai suka hadu da juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.