Isa ga babban shafi

Damben Boxing: Nasarar Fury kan Ngannou ta bar baya da kura

Fafatawar da aka yi tsakanin fitaccen dan damben boxing Tyson Fury, da Francis Ngannou tsohon dan wasan UFC da ya kasance bako a fagen na boxing, ta bar baya da kura, inda aka samu rarrabuwar kai tsakanin magoya baya da sauran masu kallo a kan sakamakon da alkalai suka bayyana.

Tyson Fury, yayin karawa da Francis Ngannou a birnin Riyad da ke Saudiya. 28 Oktoba, 2023.
Tyson Fury, yayin karawa da Francis Ngannou a birnin Riyad da ke Saudiya. 28 Oktoba, 2023. REUTERS - AHMED YOSRI
Talla

Sai da aka kai turmi na 10 yayin kece rainin da aka yi a Saudiya, duk da cewar karo na farko kenan da Nagannou ya shiga damben na boxing, inda ya kuma fafafata da fitacce a ajin masu nauyi, wato Tyson Fury.

Bayan kammala turmi na goman ne alkalan damben suka bayyana cewar Fury ne ya samu nasara kan Nagannou ta hanyar zarta shi wajen cin makin da ake kwatantawa da naushin da suka rika kirbawa juna.

Sakamakon dai bai yi wa wasu da dama dadi ba, la’akari da cewar yayin zagaye na uku a fafatawar da suka yi, sai da Ngannou ya kai Fury kasa saboda karfin naushin da ya gabza masa.

Sai dai cikin sakamakon da suka fitar, alkalan karawar sun ce sau 71 Fury ya naushi Ngannou, yayin da shi kuma tsohon mafadacin na gasar UFC ya naushi abokin hamayyarsa sau 59, kodayake a cewar alkalan, jerin naushi karfafa har sau 37 Ngannou ya gabzawa Fury, yayin da shi kuma ya samu nasarar kai jerin dukan mai karfi sau 32 kan abokin hamayyar tasa.

Daga karshe dai alkalai sun bai wa Tyson Fury maki 95, yayin da Francis Ngannou ya samu maki 94.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.