Isa ga babban shafi

Fury ya nemi a biya shi fam miliyan 500 kafin sake komawa dambe

Fitaccen dan damben boxing a duniya dan asalin Birtaniya Tyson Fury, ya bayyana cewa sai an biya shi fam miliyan 500 muddin ana bukatar ya sake komawa fagen wasan dambe.

Tyson Fury, fitaccen dan damben boxing na duniya ajin masu nauyi.
Tyson Fury, fitaccen dan damben boxing na duniya ajin masu nauyi. © REUTERS/Ahmed Yosri
Talla

Fury mai shekaru 33, na cigaba da nanata cewar zai yi ritaya daga wasan damben boxing bayan da ya samu nasarar doke Dillian Whyte a filin wasa na Wembley a cikin watan Afrilu.

Gwarzon gasar damben ajin masu nauyi ta WBC ya yi wa magoya bayansa bazata a lokacin da ya bayyana matakinsa na yin ritaya, sai dai daga bisani ya ce a shirye yake ya koma fili domin fafata wasa na musamman da  Anthony Joshua, idan har za a biya shi fam miliyan 200.

A halin yanzu kuma Tyson Fury ya daga darajar kudin da ya nema zuwa fam miliyan 500.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.