Isa ga babban shafi

Fury ya kare kambunsa na WBC bayan lallasa Whyte

Tyson Fury dan kasar Birtaniya ya lallasa Dillian Whyte gami da doke shi a zagaye na shida na fafatawar damben boxing da suka yi a ranar Asabar, nasarar da ta bashi damar ci gaba da rike kambunsa na ‘yan damben duniya ajin masu nauyi na WBC.

Tyson Fury yayin karawa da Dillian Whyte a damben boxing ajin masu nauyi, ranar Asabar 23 ga watan Afrilu.
Tyson Fury yayin karawa da Dillian Whyte a damben boxing ajin masu nauyi, ranar Asabar 23 ga watan Afrilu. Action Images via Reuters - ANDREW COULDRIDGE
Talla

Fury da Whyte sun fafata ne a gaban ‘yan kallo 94,000 a filin wasa na Wembley da ke Ingila.

Ana kaiwa zagaye ko turmi na shida ne dai Fury narkawa Whyte naushin da ya tilasta masa kaiwa kasa, kuma duk da cewar Whyte ya yi kokarin mikewa don cigaba da fafatawar, alkalin wasa ya yanke hukuncin kawo karshen damben.

An danganta Fury wanda bai taba yin rashin nasara ba, da zai kara da wanda yayi nasara a fafatwar da za a yi tsakanin Anthony Joshua da Oleksandr Usyk na kasar Ukraine.

Sai dai dan wasan mai shekaru 33 ya ce karawar da ya yi da Whyte na iya zama ta karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.