Isa ga babban shafi

Joshua na fatan dawo da martabarsa bayan karawa da Ngannou a Saudiya

Fitaccen dan damben boxing Anthony Joshua, ya bayyana fatan cewa kece rainin da zai yi da tsohon dan wasan fadan komai da ruwanka na UFC,Francis Ngannou, zai maido da martabarsa ta zama zakaran ‘yan damben zamani ajin masu nauyi na duniya.

Fitaccen dan damben boxing Anthony Joshua da takwaransa kuma tsohon dan wasan fadan komai da ruwanka na UFC, Francis Ngannou.
Fitaccen dan damben boxing Anthony Joshua da takwaransa kuma tsohon dan wasan fadan komai da ruwanka na UFC, Francis Ngannou. © Montage RFI - AFP - AP/Rebecca Blackwell
Talla

Joshua zai kara da Ngannou wanda shi ne karo na biyu da zai dambace ne a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, a ranar 8 ga watan Maris.

Ngannou dan Kamaru ya fafata dambensa na farko ne a watan Oktoban da ya gabata inda ya bayar da mamaki, musamman bayan da ya kai fitaccen dan dambe ajin masu nauyin Tyson Fury zuwa kasa wanwar saboda karfin naushin da ya kirba masa, ko da yake bayan tattara jimillar maki, alkalan wasa suka bayyana Furyn a matsayin wanda yayi nasara yayin karawar a Saudiya.

Anthony Joshua da ke neman maido da martabarsa a fagen dambe, ya yi nasara a dukkanin wasanni uku da ya fafata a shekarar 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.