Isa ga babban shafi

Joshua ya ce yanzu ne lokaci mafi hatsari da wani zai dambace da shi

Anthony Joshua  ya ce yanzu ne lokaci mafi hatsari da wani zai dambace da shi, inda ya ce damben boksin ajin masu nauyi na cikin wani hali mara armashi.

Anthony Joshua shahararren dan  damben Boxing.
Anthony Joshua shahararren dan damben Boxing. Andrew Couldridge/Reuters
Talla

Dan damben boksin din mai shekaru 33 zai dambace da dan kasar Amurka, Jermaine Franklin  a filin wasa na O2 Arena a birnin Landan ranar Asabar din nan.

Rabon Joshua da shiga da’irar boksin tun bayan da ya sha dukan kawo wuka a hannun zakaran damben boksin na yanzu,  Oleksandr Usyk a watan Agusta.

Joshua ya bayyana farin cikin damar da ya sake samu na fafatawa a filin dambe, inda kuma ya bayyana mamakin yadda har yanzu masu rike da kambunan damben boksin ajin masu nauyi ba  su gwabza ba har yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.