Isa ga babban shafi

Arsenal ta karbi jagorancin teburin Firimiya bayan nasara kan Luton

Arsenal ta koma jagorancin teburin Firimiyar Ingila bayan nasarar doke Luton da kwallaye 2 da nema a daren jiya Laraba, ko da ya ke haduwar Liverpool da Shiffield United ce za ta tabbatar da ci gaba da zaman tawagar ta Mikel Arteta a saman teburin ko akasin haka.

'Yan wasan Arsenal bayan nasara a karawarsu.
'Yan wasan Arsenal bayan nasara a karawarsu. AP - Kin Cheung
Talla

Arsenal ta doka wasan na jiya ne ba tare da dan wasanta mafi zura kwallo ba, wato Bukayo Saka wanda ya samu rauni yayin haduwarsu Manchester City a karshen mako.

Yanzu haka Arsenal na jagoranci ne da maki 68 tazarar maki guda tal tsakaninta da Liverpool a gurbin ta biyu da kuma Manchester City a gurbin ta 3, ko da ya ke tawagar Jurgen Klopp na da wasa guda a hannu.

Luton FC ta doka wasan na jiya ne tare da tarin ‘yan wasanta ba, wanda ya tilasta mata dakko kananun ‘yan wasa daga kwalejin horar da ‘yan wasa na kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.