Isa ga babban shafi

Ina da kwarin gwiwar Manchester City za ta lashe kofin Firimiya a bana- Shearer

Fitaccen tsohon dan wasan Ingila Alan Shearer da ya shahara wajen sharhi kan wasanni ya yi hasashen cewa duk da halin da teburin Firimiya ke ciki a yanzu, yana da yakinin Manchester City ce za ta sake lashe kofin gasar a bana.

'Yan wasan Manchester City bayan nasarar dage kofin Firimiyaa kakar wasan da ta gabata.
'Yan wasan Manchester City bayan nasarar dage kofin Firimiyaa kakar wasan da ta gabata. AP - Martin Rickett
Talla

A wata zantawarsa Shearer wanda ya halarci haduwar City da Arsenal a karshen mako, ya ce har yanzu babu wata kungiya tsakanin Liverpool da ke jagoranci teburin gasar da Arsenal mai biye da ita, da ke da zarrar iya lashe kofin na firimiya a bana.

A cewar Shearer duk da cewa ‘yan wasan Pep Guardiola basa taka leda yadda ya kamata, amma abin tunawa shi ne wannan ne wasa na 23 a dukkanin gasa da suka doka ba tare da anyi nasarar doke su ba.

Bayan tashi wasa babu kwallo tsakaninta da Arsenal, yanzu haka City na matsayin ta 3 ne a teburin gasar kasa da Arsenal da ke matsayin ta 2 da banbancin maki guda.

Wani babban kalubale da City ke fuskanta a wannan kaka shi ne har zuwa yanzu bata iya doke ko da guda cikin manyan kungiyoyin firimiya 5 a wannan kaka ba, sai dai duk da haka Shearer ya ce akwai kwarin gwiwar su iya sauya teburin Firmiyar yayin haduwarsu da Aston Villa a wannan Laraba.

A cewar Shearer babban kwarin gwiwar da City ke da shi a tseren lashe kofin shi ne, Firimiyar ba bakuwarta ba ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.