Isa ga babban shafi

Arsenal ta barar da damar karbar jagorancin teburin Firimiya

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta rasa damar zuwa saman teburin Firimiya bayan shan duka a hannun West Ham United da kwallaye 2 da nema har a gidanta a daren jiya Alhamis, matakin da ya bai wa Liverpool damar ci gaba da jagorancin teburin da tazarar maki 2 tsakaninsu.

Mai horas da kungiyar Arsenal  Mikel Arteta.
Mai horas da kungiyar Arsenal Mikel Arteta. AP - Jon Super
Talla

Duk da yadda ‘yan wasan na Arsenal suka yi iyakar kokarinsu wajen ganin sun farke kwallayen ciki har da wani kwakkwaran farmakin Bukayo Saka gabanin tafiya hutun rabin lokaci dama yunkurin Gabriel Martinelli da Gabriel Jesus haka dai suka hakura aka tashi wasan ba tare da samun kwallo ba.

Tun a minti na 13 gabanin tafiya hutun rabin lokaci West Ham ta zura kwallo guda ta hannun Soucek da taimakon Bowen yayinda ta kara kwallo ta biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a minti na 55.

In banda barar da fenaritin da Benrahma ya yi a karin lokacin da aka yi yayin karawar ta jiya, da tuni za a lallasa Arsenal din ne da kwallaye 3 da nema.

Shi kansa tsohon dan wasan West Ham da Arsenal ta sayo a kakar da ta gabata Declan Rice wanda wannan ne karon farko da ya tunkari tsohuwar kungiyar tasa ya yi kwararan yunkurin zura kwallo amma kuma mai tsaron raga Alphonse Areola na tare kwallon.

A bangaren Hammers kuwa wannan ne wasa na 3 a jere da ta yi nasara karkashin gasar ta Firimiya wanda ya basu damar kara makinsu zuwa 33 a matsayin na 6 a teburin, maki mafi yawa da kungiyar ta taba samu a irin wannan lokaci da aka ci rabin wasannin kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.