Isa ga babban shafi

Reece James zai sake yin jinyar rauni makwanni bayan dawowa fili

Kyaftin din Chelsea Reece James ya sake samun rauni a cinya, raunin da likitoci ke cewa zai sake shafe watanni ya na jinya, duk da cewa bangaren dan wasan da ita kanta kungiyar har zuwa yanzu ba su sanar da tsawon lokacin da dan wasan zai dauka gabanin murmurewa ba.

Reece James na Chelsea.
Reece James na Chelsea. POOL/AFP
Talla

James wanda ko a wasan da Everton ta lallasa Chelsea da kwallaye 3 da nema a Goodison Park makwanni 2 da suka gabata, sai da aka fitar da shi daga karawar tun ana minti na 26 da faro wasa, ya ce yana ganin tsana daga magoya baya saboda yawan raunin da ya ke samu.

Wasan dai shi ne karon farko da James ya dokawa Chelsea tun bayan ranar 25 ga watan Nuwamba, sakamakon jinyar da ya yi wadda ta sanya shi rasa wasanni har guda 8.

Dan wasan mai shekaru 24 da ke sahun zaratan da Chelsea ke tinkaho da su, yawan raunin na sa ya haddasawa kungiyar gagarumin koma baya.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Intagram, Reece James ya nemi afuwar magoya bayan Chelsea inda ya ce yanzu haka anyi masa tiyata sai dai jinyarsa a wannan karon za ta yi tsawo fiye da wadda ya yi a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.