Isa ga babban shafi

Cole Palmer ya taimakawa Chelsea raba maki da Manchester City 4 - 4

Cole Palmer ya taimakawa Chelsea raba maki da masu rike da kofin Frimiya Manchester City a wasan mako na 12 na gasar Ingila da suka fafata jiya Lahadi a Stamford Bridge, inda suka tashi 4-4.

'Yan wasan Chelsea na murna bayan Cole Palmer ya zura kwallo ta hudu a wasan gasar firimiya ta Ingila tsakanin Chelsea da Manchester City a filin wasa na Stamford Bridge da ke Landan, Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, 2023. (AP Photo/Ian Walton)
'Yan wasan Chelsea na murna bayan Cole Palmer ya zura kwallo ta hudu a wasan gasar firimiya ta Ingila tsakanin Chelsea da Manchester City a filin wasa na Stamford Bridge da ke Landan, Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, 2023. (AP Photo/Ian Walton) AP - Ian Walton
Talla

Saura kiris a tashi wasan ne wato a minti na 90 Chelsea ta samu fenariti, inda Palmer ya doka kwallon ya fada raga.

Erling Haaland ne ya fara ci wa City kwallo a minti na 25 da bugun fenariti, sai dai minti biyar tsakani, Chelsea ta farke ta hannun Thiago Silva.

Dan wasan Manchester City Bernardo Silva, na kalubalantar kwallon da Cole Palmer ya zura wa Chelsea a wasan gasar Firimiya ta Ingila tsakanin Chelsea da Manchester City a filin wasa na Stamford Bridge a London, Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, 2023. (AP Photo/Ian Walton)
Dan wasan Manchester City Bernardo Silva, na kalubalantar kwallon da Cole Palmer ya zura wa Chelsea a wasan gasar Firimiya ta Ingila tsakanin Chelsea da Manchester City a filin wasa na Stamford Bridge a London, Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, 2023. (AP Photo/Ian Walton) AP - Ian Walton

Daga nan Chelsea ta kara na biyu ta hannun Raheem Sterling, sai dai daf da za’a tafi hutun rabin lokaci City ta farke ta hannun Manuel Akanji.

Haalan ya ci kwallo biyu

Minti biyu bayan da aka dawo daga hutu Erling Haaland ya kara na uku kuma na biyu da ya zura a raga a wasan, sai kuma Nicolas Jackson ya farke wa Chelsea a minti na 67.

Erling Haaland na Manchester City yana murna bayan ya ci kwallon farko da kungiyarsa ta buga a gasar firimiya ta Ingila tsakanin Chelsea da Manchester City a filin wasa na Stamford Bridge da ke Landan, Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, 2023. (John Walton/PA ta hanyar AP)
Erling Haaland na Manchester City yana murna bayan ya ci kwallon farko da kungiyarsa ta buga a gasar firimiya ta Ingila tsakanin Chelsea da Manchester City a filin wasa na Stamford Bridge da ke Landan, Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, 2023. (John Walton/PA ta hanyar AP) AP - John Walton

Sauran minti hudu a tashi daga wasa Rodrigo Hernandez ya ci wa City kwallo na hudu.

Palmer ya fidda kitse a wuta

Daga nan ne fa Palmer ya ramawa Chelsea ana daf da karkare wasa.

Sai dai duk da wannan sakamakon City ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da maki 28 da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool ta biyu da kuma Arsenal ta uku, Tottrnham ke biye musu a matsayin ta hudu a saman teburin Firimiyar Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.