Isa ga babban shafi

Erling Haaland ya lashe kyautar gwarzon Firimiya na bana

Erling Haaland na Manchester City ya lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara na Firimiyar Ingila yayinda Bukayo Saka na Arsenal shi kuma ya lashe kyautar gwarzon matashin dan wasa mafi hazaka.

Erling Haaland, na Manchester City.
Erling Haaland, na Manchester City. © AFP - DARREN STAPLES
Talla

Haaland dan Norway mai shekaru 23 ya taimakawa tawagar Pep Guardiola wajen lashe kofin Firimiya da na FA da kuma zakarun Turai a kakar da ta gabata.

A dukkanin wasanni Haaland ya yi nasarar zura kwallaye 52 cikin kakar da ta gabata wanda ya ba shi damar shiga gaban Kevin de Bruyne da John Stones baya ga shi Saka na Arsenal da kuma Martin Odegaard dama Harry Kane na Tottenham da yanzu ya koma Bayern Munich.

A jawabinsa bayan karbar kyautar, Haaland ya ce matukar girmamawa ce a gare shi da aka zabe shi wajen samun wannan kyauta ta gwarzon Firimiya.

A cewar matashin dan wasan kakar da ta gabata na cike da tarihi kuma ya na fatan maimaita makamantan ta, lura da cewa bai taba tsammanin iya lashe kofuna har 3 a kaka guda ba.

Daga Borussia Dortmund ne Manchester City ta sayo Haaland kan fam miliyan 51 cikin watan Yunin shekarar 2022.

Shi ma Bukayo Saka ya yi wannan nasarar ne bayan doke takwarorinsa irin su Moises Caicedo da ya koma Chelsea daga Brighton a baya-bayan nan da kuma Jacob Ramsey na Aston Villa da Gabriel Martinelli na Arsenal da ma Evan Ferguson na Brighton.

A jumulla Saka dan Ingila mai shekaru 21 ya zura kwallaye 14 yayinda ya taimaka aka zura wasu 11 cikin kakar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.