Isa ga babban shafi

Chelsea ta yi watsi da tayin Manchester United kan Mason Mount

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi watsi da tayin fam miliyan 40 da Manchester United ta yi kan dan wasanta Mason Mount.

Dan wasan gaba na Ingila da ke taka leda da Chelsea, Mason Mount.
Dan wasan gaba na Ingila da ke taka leda da Chelsea, Mason Mount. © Phil Noble/AP
Talla

Erik ten Hag dai na fatan kawo Mount mai shekaru 24 OldTrafford don cike masa gibin da ya ke da shi a bangaren ‘yan wasan gaba masu zura kwallo.

Sai matashin dan wasan na Ingila na da sauran shekara guda a kwantiragin da ke tsakaninshi da Chelsea wanda ya san kungiyar ke neman fam miliyan 70 gabanin rabuwa da shi farashin da United ke ganin ya yi matukar tsada kan dan wasan.

Wannan mataki na United game da farashin Mount shi ke fayyace cewa abu ne mai wuya kungiyar ta iya sayen Harry Kane na Tottenham da aka sanyawa farashin fam miliyan 100 duk kuwa da yadda ake jita-jitar ta fara tattaunawa da dan wasan.

Mount wanda ya samu horo a kwalejin ‘yan wasa ta Chelsea makaranta da ya faro tun yana shekaru 6 da haihuwa, ya shafe tsawon lokaci matsayin aro a kungiyoyin kwallon kafa na Derby County da Arnhem gabanin fara dokawa Chelsea wasa a shekarar 2019, inda cikin kakar wasa 3 ya taimakawa kungiyar kashe kofin zakarun Turai ko da yake ya gamu da matsala a wannan kaka sakamakon doguwar jinya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.