Isa ga babban shafi

Manchester United na son rabuwa da Jadon Sancho

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kagu matuka ta raba gari da Jadon Sancho dai dai lokacin da Aston Villa ke nuna sha’awar sayenshi ko da ya ke da yiwuwar akai ruwa rana game da farashin da United ta sanya kan matashin dan wasan na Ingila.

Dan wasan Ingila Jadon Sancho da Manchester United ta sayo daga Borussia Dortmund.
Dan wasan Ingila Jadon Sancho da Manchester United ta sayo daga Borussia Dortmund. AP - Michael Sohn
Talla

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa bayan shekara 2 a Old Trafford, kungiyar na son raba gari da Sonko wanda ta ke neman yuro miliyan 70 akansa farashin da majiyoyin ke cewa Villa ta yi tirjiya akai.

Kungiyar ta birnin Birmingham ta bayyana cewa farashin Sancho mai shekaru 23 dududu ba zai haura yuro miliyan 55 da rabi ba, kuma idan har United na son cinikin da gaske akwai bukatar ta sauke farashin.

Jaridar wasanni ta Mail ta musanta jita-jitar cewa Tottenham na neman Sancho sai dai tace tabbas Villa wadda yanzu haka ke kokarin kawo Monchi daga Sevilla ta nuna sha’awar sayen matashin dan wasan.

Sancho wanda ya horu daga kwalejin wasanni ta Manchester City shekaru 2 da suka wuce ne Manchester United ta kwallafa rai wajen sayo shi daga Borussia Dortmund kan yuro miliyan 85.

Cikin wasanni 79 da ya dokawa United tun bayan sayo shi, kwallaye 12 kadai ya iya zurawa yayinda ya taimaka aka zura wasu 6 lamarin da bai yiwa Erik ten Hag dadi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.