Isa ga babban shafi

Makomar Maguire a Manchester United na cike da rashin tabbas

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Erik ten Hag ya ce dan wasan baya na club din Harry Maguire na da damar zabarwa kansa makoma a cikin tawagar.

Dan wasan bayan Manchester United Harry Maguire.
Dan wasan bayan Manchester United Harry Maguire. AFP/File
Talla

Maguire wanda ke matsayin mai tsaron baya mafi tsada, wasanni 16 kadai ya doka cikin wannan kaka karkashin manaja ten Hag, bayan da kocin a yanzu ya zabi amfani da Lisandro Martinez da Raphael Varane a baya.

Yayin zantawar ten Hag da jaridar wasanni ta Times, manajan ya ce shi kansa baya yi masa dadi rabuwa da Maguire lura da yadda dan wasan ke jajircewa wajen atisaye kuma shi kansa baya jin dadin abin da ke faruwa da shi.

A cewar ten Hag, Maguire har yanzu shi ne kyaftin din United kuma ya na bayar da gagarumar gudunmawa amma zabi ya rage nashi idan ya ga halin da ake ciki bai yi masa ba yana damar zabar abin da yaga ya fi dacewa da shi.

Maguire mai shekaru 30 ya tafka kura-kuran da suka sanya United a matsala cikin wannan kaka, ciki kuwa har da kuskuren da ya kaisu ga shank aye hannun Sevilla da kwallaye 3 da nema karkashin gasar Europa.

A shekarar 2019 ne Manchester United ta sayi Maguire kan farashin yuro miliyan 80 matsayin dan wasan baya mafi tsada a tarihi kuma kwantiraginsa zai kai shi ne har shekarar 2025.

Duk  da cewa a doguwar hirar ten Hag bai bayyana ko Maguire zai ci gaba da zama a kungiyar ba, amma tsohon manajan na Ajax ya jaddada cewa basu da shirin rabuwa da mai tsaron ragar kungiyar David de Gea a wannan kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.