Isa ga babban shafi

Dalilin da yasa Manchester United ta ajiye Harry Maguire a benci

Harry Maguire ya yi atisaye sau daya kacal a Manchester United tun bayan dawowarsa daga gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Qatar.

Harry Maguire
Harry Maguire AFP
Talla

An bayyana cewa za a maye gurbin Maguire a wasan da Manchester za ta ziyarci Nottingham Forest, bayan da ya gaza buga wasan da suka doke Burnley kwanaki shida da suka gabata ba saboda rashin lafiya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa dan wasan mai shekaru 29 yana fama da rashin lafiya, abin da ya sanya Maguire samun kansa a benci a wasan farko na Premier cikin kwanaki 44.

Raphael Varane ya dawo United amma har yanzu Erik ten Hag yana horas da kungiyar ba tare da Lisandro Martinez ba bayan wasan karshe na gasar cin kofin duniya inda shima dan wasa Victor Lindelof kef ama da rashin lafiya.

Maguire ya gaza samun saukin rashin lafiyar da yake fama da ita, kuma wata majiya ta ce kyaftin din na United na bukatar kwanciya domin samun kulawar likitoci sosai, amma Maguire ya ki amincewa ya zauna wurin ma’aikatan jinya.

Dan wasan da ke zaman kwantaragin sama da Yuro miliyan 80 sau daya kenan aka ganshi a gasar Premier tun bayan da United ta lallasa Brentford da ci 4-0 a ranar 13 ga watan Agusta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.