Isa ga babban shafi

Kofin gasar Premier ya koma hannun Manchester City - Guardiola

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce ‘yan wasansa sun nuna wa duniya cewar, za su iya fidda kai daga kunya ta hanyar samun nasara, ko da kuwa kalubalen da ke gabansu babba ne, musamman idan ya zamana  ba su da wani  zabi illa samun nasara a wasan da za su fafata.

Kocin Manchester City Pep Guardiola
Kocin Manchester City Pep Guardiola AP - Alastair Grant
Talla

A daren ranar Laraba ne dai ‘yan wasan City suka lallasa takwarorinsu na Arsenal da kwallaye 4-1 a filin wasa na Ettihad.

A lokacin da yake tsokaci bayan wasan da suka fatata, Guardiola ya kara da cewar, a halin yanzu kofin gasar Premier na hannun Manchester City

Nasarar dai ta bai wa kungiyar damar rage tazarar da ke tsakaninta da Arsenal zuwa maki biyu kacal, yayin da kuma take da kwantan wasanni biyu da za ta buga, abinda  ke nufin kungiyar na da ragowar  wasanni 7, kafin a karkare gasar Premier ta bana.

A halin yanzu Manchester City na da damarmakin lashe kofuna uku a kakar wasa  ta bana, da suka hada da na FA, na Premier da kuma na gasar Zakarun Turai, wadda z ata kara da Real Madrid a wasan kusa da na karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.