Isa ga babban shafi

Manchester City na da kwanten wasa biyu, gabanin wasanta da Arsenal

Pep Guardiola da Mikel Arteta dukkanin su sun tabbatar da cewa, kasancewa a saman teburi tsakanin Manchester City da Arsenal ba shine zai tabbatar da lashe gasar Premier ba.

Pep Guardiola da Mikel Arteta kenan
Pep Guardiola da Mikel Arteta kenan © Eurospost
Talla

Arsenal wadda ke jagorantar teburin gasar tazarar maki biyar ne tsakanin ta da kungiyar Pep Guardiola kafin wasan da za ayi kenan na ranar Laraba a filin wasa na Etihad.

Sai dai City da ke a matsayi na biyu na da kwantan wasanni biyu yayin da Arsenal su kuma suka yi canjaras a wasanni uku a jere.

"Yana da mahimmanci, amma ba za a yanke hukunci ba saboda akwai wasanni da yawa da za a buga," in ji kocin City Guardiola.

Mutanen biyu sun yi aiki tare a City kafin Arteta ya zama kocin Arsenal a 2019, amma Guardiola ya ce babu wani abu da ya canza a dangantakar su.

Arsenal dai ta fuskanci shan kashi a hannun City a gasar da gasar cin kofin FA a kakar wasa ta bana kuma Arteta na tsammanin wani wasa mai cike da sarkakiya da ke fuskantar sa a halin yanzu.

Arsenal wadda ta lashe gasar Premier ta karshe a shekara ta 2004, ta yi kunnen doki 3-3 da Southampton wacce ke mataki na karshe a ranar Juma’a, bayan da ta yi nasara a kan West Ham da Liverpool da ci biyu da nema.

Guardiola ya ce tsohon mataimakinsa ya taimaka wajen daukar Gunners zuwa wani mataki na daban.

Ya ce "Arsenal na da cikakkun bayanai masu ban mamaki game da yadda ‘yan wasan ke sarrafa kwallo, 'yan wasan da suke zaba a kungiyar suna da kwarewa sosai," in ji Guardiol.

"Mikel Arteta ya kawo su zuwa wani mataki na daban; suna da matukar fa'ida da kuma kwarewa."

Arteta ya tabbatar da cewa dan wasan tsakiya Granit Xhaka, wanda bai buga wasan da suka yi da Southampton ba, babu tabbacin zai kasance cikin tawagar da za ta fuskanci City, yayin da dan wasan baya William Saliba ya nuna ke ci gaba da murmurewa daga raunin da ya samu a bugun daga kai sai mai tsaron gida a gasar Europa da suka yi rashin nasara a hannun Sporting Lisbon a watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.