Isa ga babban shafi

Rashford ya kai Man U na hudu a teburi, Newcastle ta lallasa West Ham da ci 5-1

Marcus Rashford ya taimakawa Manchester United zuwa na ‘yan hudun saman teburi a gasar Premier bayan da Red Devils ta doke Brentford da 1-0 a ranar Laraba, yayin da Newcastle ta yi wa West Ham dukan kawo wuka da 5-1 ta koma matsayi na uku a teburi.

Dan wasan Manchester United Marcus Rashford lokacin da yake murnar zura kwallo a 2019
Dan wasan Manchester United Marcus Rashford lokacin da yake murnar zura kwallo a 2019 AFP/Archivos
Talla

Callum Wilson da Joelinton kowannen su ya zura kwallaye biyu a ragar Magpies, abin da ya basu damar dara United da banbancin yawan kwallaye saboda kowa na da maki 53.

Yanzu dai dukkanin bangarorin biyu na da maki uku a kan Tottenham da kuma wasa a hannun ita Spurs a fafutukar su na neman gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai na kakar wasa mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.