Isa ga babban shafi

Tottenham ta nuna bajinta bayan doke Manchester City da kwallo 1 mai ban haushi

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta yi rashin nasara a hannun Tottenham da kwallo daya mai ban haushi, rashin nasarar da ya hana ta samun damar rage tazarar da ke tsakaninta da jagorar firimiya Arsenal wadda itama a karshen mako ta yi rashin nasara a hannun Everton da kwallo dayan mai ban haushi.

Wannan ne karo na 5 da Manchester City ke zuwa gidan Tottenham ba tare da ta samu maki ko kwallo ba.
Wannan ne karo na 5 da Manchester City ke zuwa gidan Tottenham ba tare da ta samu maki ko kwallo ba. Action Images via Reuters - MATTHEW CHILDS
Talla

Kafin wasan dai akwai tsammanin lokaci yayi da tawagar ta Pep Guardiola za ta rage tazarar da ke tsakaninta da Arsenal amma kuma sai Tottenham ta yi tirjiya tare da hana ta rage nisan da ke tsakaninta da kofin na firimiya.

Dan wasan gaba na City Riyad Mahrez ya yi kwararan yunkuri don ganin ya farke kwallon amma ya rika gamuwa da tirjiya.

Rashin nasarar ta City na nuna cewa wannan ne karo na biyar da da tawagar Pep Guardiola ke yin tattaki zuwa Tottenham ta fito hannu fayar ba tare da maki ko kwallo ba.

Nasarar ta Tottenham wadda ta karkare wasa da mutum 10 bayan bai wa Cristian Romero jan kati yanzu haka tazarar da ke tsakaninta makwabciyarta Newcastle wadda ke matsayin ta 4 a teburin firimiyar ya ragu zuwa maki guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.