Isa ga babban shafi

Chelsea ta gana da tsohon kocin Bayern Munich Julian Nagelsmann

Chelsea ta tattauna da tsohon mai horas da Bayern Munich Julian Nagelsmann kan yiwuwar daukarsa a matsayin sabon kocinta na dindindin.

Tsohon mai horas da Bayern Munich Julian Nagelsmann
Tsohon mai horas da Bayern Munich Julian Nagelsmann AP - Martin Meissner
Talla

A watan Maris Bayern Munich ta salami Nagelsmann, kasa da shekaru biyu bayan kulla yarjejeniya da shi, kuma har yanzu kocin bai samu aikin horas da wata kungiyar ba.

Duk da tuntubar Nagelsmann da suka yi, bayanai sun ce shugabannin Chelsea na cigaba da laluben wanda ya fi  dacewa su bai wa aikin koras da kungiyar ta su, daga cikin wadanda suke shirin tuntuba kuma har da tsohon mai horas da Barcelona Luis Enrique.

A halin yanzu dai Frank Lampard ne yake rike da aikin horas da Chelsea amma na wucin gadi, bayan da kungiyar ta sallami Graham Potter kasa da watanni  bakwai, bayan da ya rabu da kungiyarsa ta Brighton  don maye gurbin Thomas Tuchel.

Dukkanin wasanni ukun da Lampard ya jagoranta dai bai samu nasara ba, abinda ya sa da dama ke ganin aikin na sa ba zai dore ba, kamar yadda ya gaza a zangon farko na jagorancin kungiyar da yayi a matsayin kocin dindindin a tsakanin watan Yulin shekarar 2019, zuwa Janairun 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.