Isa ga babban shafi

Lampard zai sake komawa Chelsea a matsayin koci na wucin gadi

Frank Lampard na shirin komawa Chelsea karo na biyu amatsayin cocin wucin gadi har zuwa karshen kakar wasa ta bana, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Frank Lampard na shirin komawa Chelsea karo na biyu amatsayin cocin wucin gadi har zuwa karshen kakar wasa ta bana, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Frank Lampard na shirin komawa Chelsea karo na biyu amatsayin cocin wucin gadi har zuwa karshen kakar wasa ta bana, kamar yadda rahotanni suka bayyana. AFP
Talla

 

Lampard, wanda Everton ta kora a farkon kakar wasa ta bana, Chelsea ta sallame shi a shekarar 2021 bayan ya shafe watanni 18 yana horarwa.

Sky Sports da The Athletic duk sun ruwaito cewa yanzu haka kulob din da Lampard na tattaunawa a kokarin ganin an nada tsohon dan wasan na Ingila da gaggawa domin jagorancin bulaguro zuwa Wolves ranar Asabar.

Chelsea na fuskantar koma baya

Chelsea ta kori Graham Potter a ranar Lahadin da ta gabata bayan da ta yi fama da bala'in da ya sa kungiyar ta zama ta 11 a teburin Premier duk da kashe sama da fam miliyan 500 (dala miliyan 623) kan sabbin 'yan wasa a kakar wasa ta farko karkashin sabbin mamallakar kungiyar.

Sai dai kuma sun tsallake zuwa matakin daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai sannan kuma za su ziyarci Real Madrid mai rike da kofin gasar a wasan zagayen farko na wasan daf da na kusa da na karshe a cikin kwanaki bakwai masu zuwa.

Lampard ya taimakawa Chelsea a baya

A cikin shekaru 13 a matsayin dan wasan Chelsea, Lampard ya lashe kofunan gasar Premier uku, gasar zakarun Turai kuma ya ci gaba da zama dan wasan da ya fi zura kwallo a raga.

Kocin mai shekaru 44, ya jagoranci Chelsea a matsayi na hudu a gasar Premier da kuma gasar cin kofin FA a kakar wasansa ta farko a Stamford Bridge.

Amma an kore shi a tsakiyar kakar wasa ta biyu kuma Chelsea ta ci gaba da lashe gasar zakarun Turai a waccan shekarar karkashin Thomas Tuchel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.