Ban ji dadin hukuncin da Chelsea ta yi min ba - Lampard
Frank Lampard ya bayyana rashin jin dadin matakin sallamarsa da Chelsea ta dauka, ba tare da ta bashi isasshen lokacin jagorantar ta zuwa samun nasarorin lashe kofuna ba.
Wallafawa ranar:
A jiya litinin Chelsea ta sanar da korar Lampard watanni 18 bayan kulla yarjejeniya da shi, saboda gaza lashe wasanni 5 cikin 8 na baya bayan nan da suka fafata a gasar Premier, duk da cewar ta kashe euro miliyan 220 wajen sayen ‘yan wasa a kakar wasa ta bana.
A halin yanzu tsohon kocin PSG Thomas Tuchel ake sa ran zai maye gurbin Lampard.
Mai horas da kungiyar Tottenham Jose Mourinho, wanda tsohon kocin Lampard ne, ya ce korar da Chelsea ta yiwa dalibin nasa ya nuna irin cin zalin hukumomin gudanarwa ko shugabannin kungiyoyin kwallon kafa da ya zama ruwan dare a wannan zamani.
A cewar Mourinho baya jin dadi a duk lokacin da wani mai horaswa ya rasa aikinsa ballanta Lampard da ya bashi gudunmawa matuka lokacin da ya horas da Chelsea.
A makon jiya shi ma kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce koka kadan ba ya jin dadin yadda Lampard ke fuskantar kalubalen rashin nasarori.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu