Isa ga babban shafi
Wasanni

Lampard na fuskantar barazanar rasa mukamin horas da Chelsea

Hukumar gudanarwar Chelsea ta gindayawa kocin kungiyar Frank Lampard sharadin cewar ya zama dole su kammala kakar wasa ta bana a tsakanin kungiyoyi 4 na farko a gasar Premier, muddin yana son cigaba da rike mukaminsa.

Frank Lampard, mai horas da kungiyar Chelsea
Frank Lampard, mai horas da kungiyar Chelsea Reuters
Talla

Jaridar UK Mirror ta ruwaito cewar a gefe guda shugabannin kungiyar ta Chelsea sun soma nazarin wanda zai maye gurbin Lampard idan ya gaza kai su ga gaci.

Wadanda ake sa ran za su iya maye kocin na Chelsea kuwa sun hada da mai horas da kungiyar RB Leipzig Julian Nagelsmann da kuma Thomas Tuchel tsohon kocin PSG, yayin da kuma aka ruwaito tsohon kocin Juventus Masmilliano Allegri na cewa, yana sha’awar horas da wata kungiya a Ingila.

A ranar Talata kungiyar Leicester City ta doke Chelsea da 2-0.

Yayin tsokaci bayan wasan da suka sha kayen ne kuma, mai horas da Chelsea Frank Lampard ya bayyana damuwa kan rashin karsashin da ya dabaibaye ‘yan wasansa, la’akari da cewar, karo na biyar kenan da suka yi rashin nasara cikin wasanni 8 na baya bayan nan da suka fafata a gasar Premier Ingila.

Idan za a iya tunawa dai a farkon watan Disamba Chelsea ce ke jagorantar gasar ta Premier, amma a yanzu ita ce ta takwas da maki 29.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.