Isa ga babban shafi

Everton na neman sabon koci na 6 cikin shekaru 5 bayan korar Lampard

Everton ta kori kocinta Frank Lampard kusan shekara guda bayan karbar aikin horas da ‘yan wasan kungiyar.

Franck Lampard
Franck Lampard Action Images via Reuters - JASON CAIRNDUFF
Talla

Matakin sallamar Lampard ya biyo bayan rashin nasarar Everton da kwallaye 2-0 a karawar da ta yi da West Ham United ranar Asabar, shank aye na 9 da kungiyar ta  fuskanta cikin wasanni 12 da ta fafata a gasar Firimiya.

Yanzu haka dai Everton ce ta biyun karshe a gasar Firimiya da maki 15 kaccal bayan buga wasanni 20, kuma ma makinta guda ne da ta karshe wato Southampton, sai  dai kawai bambancin yawa kwalaye.

A watan Janairun 2022 tsohon dan wasan tsakiya na Ingila kuma tsohon kocin Chelsea Lampard, ya maye gurbin Rafael Benitez a lokacin da Everton ke mataki na 16 a gasar Firimiya, kuma a wacccar kakar wasa Lampard ya taimaka mata wajen kaucewa fadawa ajin ‘yan dagaji.

A halin yanzu dai Everton tana neman kocin dindindin na shida cikin shekaru biyar Kenan bayan sallamar na yanzu.

Wasu rahotanni na cewar kunggiyar ta Everton na kan kokarin jan ra'ayin tsohn dan wasan Manchester United Wayne Rooney don maye gurbin Lampard.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.