Isa ga babban shafi

Matsalolin Chelsea ba na warwarewa cikin kwana daya ba ne - Lampard

Sabon mai horas da ‘yan wasan Chelsea na wucin gadi Frank Lampard ya ce Matsalolin da kungiyar ke fuskanta ba’abin da za ‘a magance su a kwana daya bane, bayan da ya fara da kafar hagu a Wolverhampton.

Sabon Manajan Chelsea Frank Lampard
Sabon Manajan Chelsea Frank Lampard POOL/AFP
Talla

Lampard wanda ya ja ragamar Chelsea a karon farko a matsayin kocin rikon kwarya, ya yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Wolves a gasar Premier ranar Asabar.

Wasanni uku kenan Chelsea ta doka a jere ba tare da ta yi nasara ba, kuma karo na 11 da ake doke ta a manyan gasa kwallan kafa a Ingila a wannan kaka.

Lampard, wanda bai da kungiya tun bayan da Everton ta sallame shi a watan Janairun 2023, ya horar da Chelsea daga Yulin 2019 zuwa Janairun 2021 kafin daga bisani ta kore shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.