Isa ga babban shafi

Hukumar FA ta fara tuhumar Kompany kan rashin ɗa'a ga alkalin wasa

Hukumar FA ta tuhumi mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Burnley Vincent Kompany bayan kalamansa biyo bayan bashi jan kati a wasan da suka yi canjaras da kwallaye 2 da 2 tsakaninsu da Chelsea ranar Asabar din da ta gabata.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Burnley, Vincent Kompany.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Burnley, Vincent Kompany. AFP/Archives
Talla

Tun farko Kompany ya kalubalanci alkalin wasa Darren England game da bugun fenaritin da ya baiwa Chelsea dama jan katin da ya baiwa mai tsaron baya Lorenz Assignon, wanda manajan ya bayyana da abin da bai kamata ba.

Bayan tashi daga wasan Kompany wanda tsohon dan wasan Belgium ne da ya taka leda da Manchester City ya koka da cewa lamarin alkalin wasanni na ci gaba da tabarbarewa a Ingila batun da ya fusata hukumar FA.

Sanarwar da FA ta fitar ta tuhumi Kompany da rashin ɗa’a yayinda ta bashi daga yanzu zuwa ranar juma’a don yi mata bayani.

Sanarwar ta ce kalmomin da Kompany ya yi amfani da su a lokacin ana minti na 40 da faro wasan ya sabawa dokokin da ladubban hukumar ta FA.

Cikin wannan kaka kaɗai dai ƴan wasan Burnley 6 aka kora daga fili a wasanni 30 wanda ya zama mafi yawa da wata kungiya ta taba gani a Firimiyar Ingila.

Yanzu haka dai Burnley na matsayin ta 19 ne a teburin na Firimiya yayinda ta ke shirin haduwa da Everton a ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.