Isa ga babban shafi

Dole Manchester United ta kara azama matukar tana fatan doke Arsenal- Klopp

A wani yanayi mai kama da zafin shan kaye, mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya gargadi takwaransa na Manchester United cewa tabbas za su sha kaye a hannun Arsenal yayin wasansu na watan gobe, matukar suka yi wasa irin wanda suka yi da Reds a jiya Lahadi.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jürgen Klopp.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jürgen Klopp. © Jon Super/AP
Talla

Yayin zantawarsa da manema labarai bayan shan kayen na jiya da ya hana Liverpool komawa gurbinta na jagorancin teburin Firimiya, Klopp ya bukaci magoya bayan tawagar ta Liverpool su kwantar da hankulansu lura da yadda ake da sauran wasanni 7 gabanin karkare kakar bana.

Manchester United na da rawar takawa wajen iya kai Liverpool ga nasarar lashe kofin, sai dai Klopp na da fargaba kan ko tawagar ta Erik ten Hag ba za ta iya kange nasarorin da tawagar Mikel Arteta ke ci gaba da samu a firimiyar ba, wanda ake ganin shi ya kawo wannan kira na Klopp da nufin zaburar da ‘yan wasan na United.

Da ake tambayarsa kan ko zai mara baya ga United a wasanta na ranar 11 ga watan Mayu, Klopp ya bayyana cewa idan har Liverpool na halin da take a yanzu ko shakka babu zai mara baya ga Red Devils.

Yanayin yadda teburin na Firimiya ya koma a yanzu ya sake nuna yadda tseren lashe kofin ya dawo sabo tsakanin manyan kungiyoyin 3, a kakar da ke matsayin takarshe da mai horarwa zai shafe a Liverpool.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.