Tsohon tauraron dambe Mike Tyson zai kara da Jake Paul a wasan baje kolin Arlington
Tsohon zakaran ajin masu nauyi Mike Tyson zai dawo fagen dambe inda zai kara da Jake Paul a wani bikin baje kolin Arlington, a Texas na kasar Amurka.Sanarwa daga masu shirya gasar a yau Alhamis,inda suka tabbatar da cewa Tyson, mai shekaru 57, da Paul za su fafata a filin wasa na AT&T da ke Arlington, a garin na Texas, gidan Dallas Cowboys na NFL, a ranar 20 ga Yuli shekarar 2024.
Wallafawa ranar:
A wata sanarwa daga Mike Tyson ,tsohon tauraron yana fatan doke abokin dambe Jake Paul da aka Haifa a ranar 17 ga watan janairu na shekara ta 1997 (ya na mai shekaru 27), a garin Cleveland, Ohio, na kasar Amurka.
Mike Tyson y ana mai bayyana farin ciki na ganin zai kasance a fagen dambe da matashi,tabbas shekaru sun ja,sai dai hakan ba zai hana shi nuna kwarewa da kuma tabbara da cewa ya na nan kan bakar sa ta fitacce a duniyar dambe.
Mike Tyson na daya daga cikin yan wasan dambe da ya kawar da ziratan yan dambe na Duniya.
A daya gefen dan’uwan Jake Paul Logan Paul ya taka muhimmiyar rawa wajen ba da jagoranci a wannan yanayin, har ma da yaƙi da dan damben zamani Floyd Mayweather a shekarar 2021.
Jake Paul duk da haka ya shiga tarihi a wannan tafiya,ya samu wasu nasarori a baya a kan kwararrun yan dambe a fafatawarsa biyu na ƙarshe tare da nasara a kan Ryan Bourland da Andre August.
A halin da ake ciki, Tyson, ana daukarsa a matsayin daya daga cikin yan damben boksin masu nauyi mafi girma a tarihi, inda ya kare wannan mataki a matsayin zakara tsakanin 1987 zuwa 1990, ya kuma lashe kambunsa na farko yana da shekaru 20 da watanni hudu da kwanaki 22 don zama zakaran dambe mafi karancin shekaru a tarihi. .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu