Isa ga babban shafi

Osimhen ya hana Barcelona nasara yayin wasanta da Napoli a gasar zakarun Turai

Victor Osimhen ya farke kwallon da Robert Lewandowski ya zura a karawarsu ta jiya Laraba yayin wasannin zagayen ‘yan 16 na gasar zakarun Turai wanda ya sanya tawagogin biyu yin kunnen doki wato kwallo 1 da 1.

Victor Osimhen ne ya farke kwallon da Robert Lewandowski ya zurawa Barcelona tun a minti na 60.
Victor Osimhen ne ya farke kwallon da Robert Lewandowski ya zurawa Barcelona tun a minti na 60. REUTERS - REMO CASILLI
Talla

Osimhen wanda haduwar ta jiya ke matsayin wasan farko da ya dokawa Napoli tun bayan watan Disamban bara sakamakon yada ya shafe fiye da wata guda ya na wakiltar kasar shi Najeriya a gasar cin kofin Afrika da aka kammala cikin watan nan, a minti na 75 ne bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ya yi nasarar zura kwallon.

Tun farko Robert Lewandowski ya zurawa Barcelona kwallonta ne a minti na 60 lura da yadda bangarorin biyu suka shafe zagayen farko na haduwar ta jiya a Italiya ba tare da zura kwallo ba.

Tawagar ta Xavi da ke fuskantar tarnaki a La Ligar Spain bayan tazarar maki 8 tsakaninta da jagora Real Madrid na fatan kai bantanta ne a gasar ta zakarun Turai kuma anga rawar ganin da ‘yan wasanta irinsu shi kansa Lewandowskin da Yamal da kuma Gundogan suka taka a haduwar ta jiya amma mai tsaron raga Alex Meret na musu tirjiya.

A bangare guda ita kanta Napoli na fama da tarin matsaloli lura da yadda kofin da take karewa na Serie A  ya cewa ya kufce mata, inda yanzu haka ta ke matsayin ta 9 a teburin gasar da maki 36 tazarar kusan maki 27 tsakaninta da Inter Milan jagorar teburin mai maki 63.

A watan gobe ne manyan tawagogin biyu za su hadu a zagaye na 2 na rukunin ‘yan 16 a Spain kuma a nan ne za a tantance wadda za ta tsallaka matakin ‘yan 8 da kuma wadda za ta tara a kaka ta gaba son samun gurbi a gasar ta cin kofin zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.