Isa ga babban shafi

Manchester United ta yi ficewa mafi muni daga gasar zakarun Turai

Manchester United ta yi ficewa mafi muni a tarihi daga gasar cin kofin zakarun Turai bayan shan kaye a hannun Bayern Munich da kwallo 1 mai ban haushi har filin wasa na Old Trafford.

Maii horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Erik Ten Hag.
Maii horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Erik Ten Hag. AP - Peter Dejong
Talla

Duk da yadda a baya aka yi hasashen Erik ten Hag ya sauya salon kungiyar musamman bayan lashe kofin lig a kakar farko da kuma zuba kudi wajen sayen tarin ‘yan wasa, alamu na nuna cewa ba ta sauya zani ba.

Idan aka kwatanta jagorancin ten Hag da na magabatansa irin Louis van Gaal da Jose Mourinho duk da cewa ya lashe kofin lig guda da Europa baya ga salon kamun ludayin Ole Gunnar Solskjaer, za a iya cewa Manchester United ta dawo inda ta ke a duk shekarun nan.

Ten Hag da kansa ne ya yi maraba da jadawalin da Manchester United ta samu kanta a ciki karkashin gasar ta zakarun Turai amma abin takaici sai ga kungiyar ta kammala a matsayin ta karshe a rukunin wanda ke kunshe da kungiyoyin Bayern Munich da Galatassaray da kuma FC Copenhagen.

Tun gabanin tashi daga wasan ne aka nemi magoya bayan United aka rasa a fili domin daya bayan daya suka rika ficwa don kaucewa ganewa idonsu mummunar faduwar kungiyar a gabansu ne.

Duk da cewa Ten Hag ya samu nasarori a wasan Lig na cikin gida amma har zuwa yanzu ya gaza rawar gani a gasar zakarun Turai.

Wasan na jiya dai na matsayin duka bayan duka domin kuwa a karshen mako ne Bournemouth ta casa United da kwallaye 3 da nema karkashin gasar Firimiyar Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.