Arsenal ta yi nasara a wasan farko, shekaru 6 bayan dawowa gasar zakarun Turai
Arsenal ta shigo gasar cin kofin zakarun Turai cikin salo, yayin da ta fara gasar da ta halarta karon farko cikin shekaru shida da kafar dama, wajen doke PSV Eindhoven da ci 4-0 a filin wasa na Emirates.
Wallafawa ranar:
Gunners sun ja ragama har aka je hutun rabin lokaci da ci 3-0 a wasan da suka fafata a arewacin birnin London.
Bukayo Saka ne ya fara cin kwallo bayan mintuna takwas, da soma wasa.
Saka ne dai ya taimakawa Arsenal ta ninka damar ta bayan mintuna 12, ta hannun kwallon da Leandro Trossard ya jefa, kafin Gabriel Jesus ya kara na uku a mintuna na 38 aka tafi huta ci uku na nema.
Mintuna na 70 wato zagaye na biyu ne Martin Odegaard ya zura kwallo na 4 da ya bai wa Arsenal damar jagorantar rukumin B.
Karon farko Arsenal da ta buga gasar Europa za ta dawo babbar gasar Turai tun daga shekarar 2016/17.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu