Isa ga babban shafi

Howe ya bukaci jajircewar 'yan wasan Newcastle gabanin haduwa da PSG

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United Eddie Howe, ya bukaci tawagarsa su cire fargaba tare da jajircewa yayin haduwarsu da PSG yau laraba a wasannin gasar cin kofin zakarun Turai da zai gudana a filin wasa na St James Park da ke London.

Kocin Newcastle United Eddie Howe
Kocin Newcastle United Eddie Howe Action Images via Reuters - Lee Smith
Talla

Newcastle wadda ta yi canjaras a haduwarta da AC Milan yayin wasanta na farko bayan dawowa gasar ta cin kofin zakarun Turai a bana, wasan ya zamar mata nasara mafi girma da ta yi kuma karon farko kenan da kungiyar ke karbar bakoncin wasa karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai tun bayan shekarar 2003 lokacin da ta doke Barcelona da kwallaye 2 da banza.

A cewar Manajan sam ba ya tunanin 'yan wasan na shi na shakkar haduwa da PSG, sai dai akwai bukatar sake nusar da su game da bukatar jajircewa a haduwar ta yau.

Gabanin wasan na yau, dan wasan Newcastle United, Kieran Trippier ya bayyana cewa dansa Jacob na fatan riko hannun tauraron Faransa Kylian Mbappe yayin shiga filin wasa na St James Park a haduwar ta yau.

A cewar Trippier yaron nashi magoyin bayan dan wasan na PSG ne, kuma zai so ya samu damar riko hannunsa zuwa fili a wasan na yau.

Cikin barkwanci, dan wasan na Ingila mai shekaru 33 ya ce yaron nashi yafi Fifita kama hannun Mbappe fiye da shi, sai dai ya bashi zabin cewa idan ya riko hannun Mbappe tofa shi karya neme shi ko da bayan tashi daga wasa.

Newcastle dai na ci gaba da haskawa a wasanninta na wannan kaka, inda aka gaza nasara kanta cikin wasanni 5 da ta doka a wannan kaka, ciki har da gagarumar nasara kan Sheffield United da kwallaye 8 da nema.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.