Newcastel ta fita daga gasar Zakarun nahiyar Turai a matakin rukuni
Damawa da ake yi da Newcastle United a gasar Zakarun nahiyar Turai ya kawo karshe a daren Laraba, bayan da AcMilan ta taso daga baya ta samu nasara a kanta a filinta na St James' Park.
Wallafawa ranar:
Newcastle ta yi mafarakin ganin kanta a zagayen sili daya kwale ne tun bayan da Joelinton ya saka kwallo a ragar Milan a minti na 33, a yayin da a daidai lokacin Borussia Dortmund ke kan gaba a wasan da take fafatwa da Paris St-Germain a Jamus.
Idan da wasannin na Jamus da Ingila sun kare a haka, Newcastle za ta haye, bisa yadda take kan gaba a dukkan karawar da ta yi da PSG, amma sai lammura suka sauya a cikin ‘yan mintoci, kafin a kai sa’a guda da ilharin wasannin, inda matashi Warren Zaire-Emery ya farke wa PSG kwallo a Jamus, a yayin da tsohon dan wasan Chelsea, Christian Pulisic ya farke wa AC Milan a Ingila.
Saura minti 6 a Karkare wasan ne aka tantance makomar Newcastle, sakamkon kwallon da dan wasan Najeriya, wanda ya shigo wa Milan daga baya, Samuel Chukwueze ya saka mata, wasa ya tashi 2 da 1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu