Isa ga babban shafi

Newcastle ta doke PSG da kwallaye 4 da 1 a gasar zakarun Turai

Dakon shekaru 20 da Newcastle ta yi gabanin dawowa gasar cin kofin zakarun Turai ya zowa kungiyar da gagarumar nasara bayan da ta yi nasarar lallasa PSG da kwallaye 4 da 1 a haduwarsu ta daren jiya Laraba a filin wasa na St James Park.

'Yan wasan Newcastle bayan doke PSG ta Faransa.
'Yan wasan Newcastle bayan doke PSG ta Faransa. AFP - FRANCK FIFE
Talla

Wasan wanda tsaffin ‘yan kwallon Newcastle da suka sha kaye a hannun Barcelona da kwallaye 2 da nema suka kalleshi a jiyan, wato wasan karshe da kungiyar ta doka a karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai shekaru 20 da suka gabata gabanin yin sallama da gasar, anga yadda magoya baya suka rika murna da raye-raye gaban mutum-mutumin Sir Bobby Robson da Alan Shearer da ke matsayin Manaja da dan wasa a wancan lokaci.   

Shekaru 2 da suka gabata ne Eddie Howe ya karbi ragamar Newcastle bayan da attjiran Saudiya suka saye ta, lokacin ta na matsayin ta 19 a teburin firimiyar Ingila tazarar maki 5 tsakaninta da iya fita daga rukunin ‘yan dagaaji.

A kakar da ya karbi Newcastle, zakakurin manajan ya yi nasarar iya tseratar da ita daga ficewa daga gasar ta Firimiyar Ingila, inda a bara kuma ya kaita sahun 'yan hudun saman teburi.

Tawagar ta Eddie Howe ta wujijjiga tauraron PSG Kylian Mbappe wanda aka gaza ganin kwazonsa a fili gabaki daya yayin haduwar ta jiya.

Masana dai na ganin Newcastle ta dawo da karsashinta ne da aka santa da shi cikin shekarun 1967, yayin da masu sharhi suka bayyana nasarar ta jiya da cewa za ta dade tana faranta zukatan magoya bayan kungiyar.

Tun gabanin fara wasan dai an ga yadda magoya bayan Newcastle suka rika reran waken jinjina ga Eddie Howe wanda suke kallo a matsayin wanda ya sauya lamarin kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.