Isa ga babban shafi

Sai mun kawo manyan 'yan wasa muddin muna son lashe Firimiyar Ingila- Arteta

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta ya amince cewar muddin kungiyar na son lashe gasar Firimiyar Ingila, toh dolenta ta nemo manyan ‘yan wasa.

Arsenal boss Mikel Arteta could win his first trophy as a manager in Saturday's FA Cup final
Arsenal boss Mikel Arteta could win his first trophy as a manager in Saturday's FA Cup final POOL/AFP
Talla

Arsenal ta taka rawar gani a kakar da ta gabata, harma da dama ke ganin wata kila ta lashe gasar a karon farko cikin kusan shekaru 20, sai dai haka bata cimma ruwa ba ganin yadda Manchester City ta yi mata kwab daya ana dab da karkare kakar.

A yanzu dai Gunners na kokarin kulla yarjejeniya da dan wasan tsakiya na West Ham Declan Rice da kuma dan wasan gaban Chelsea Kai Havertz.

Jinyar raunin da dan wasan Arsenal William Saliba ya yi fama da ita, na daga cikin manyan dalilan da ake ganin sun sanyata rashin samun nasarar lashe gasar a kakar da ta gabata.

Duk da cewar Arsenal ta samu tikitin zuwa gasar zakarun Turai a kaka mai zuwa, Arteta ya ce akwai ciwo yadda suka gaza samun nasarar lashe gasar Firimiya.

Ya ce dole ne su shirya don tunkarar abokan hamayyar su, domin suna da ‘yan wasa masu kwarewa ga kuma gwarzon mai horaswa da ake ji da shi a duniya da suke da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.